(ABNA24.com) Gwamnatin kasar ta Venezuela ta sanar da cewa za ta kai gwamnatin Amurka zuwa kotun manyan laifuka ta duniya saboda takunkuman da ta kakaba ma ta.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne mahukuntan Amurkan su ka sanar da kakaba sabbin takunkumai akan wasu kamfanoni na kasar Mexico da kuma wasu daidaikun mutane wadanda Amurkan ta zarga da cewa suna yin mu’amalar kasuwanci da cinikayyar man fetur da Venezuela.
Ministan harkokin wajen kasar Venezueal Jorge Arreaza ta rubuta a shafinsa na Twitter cewa; Washington tana kara takurawa Venezuela, tana kuma zaton cewa ba za mu iya fitar da man fetur dinmu ba, sun kuma bar mutanen kasar Venezuela ba tare da abinci ba ko magani ko mai.”
Ministan harkokin wajen na Venezuela ya kara da cewa; “ Dole MDD wacce ta kunshi kasashe da dama ta mayar da martani, kuma za mu je koton manyan laifuka ta duniya akan wannan batun.”
/129
20 Yuni 2020 - 09:24
Lambar labari: 1048232
Gwamnatin kasar ta Venezuela ta sanar da cewa za ta kai gwamnatin Amurka zuwa kotun manyan laifuka ta duniya saboda takunkuman da ta kakaba ma ta.
X